Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani babban jami'in Yankin HK ya yi kira da a zauna lafiya don ci gaba da rike masu basira a yankin
2019-12-01 17:09:44        cri
Wani babban jami'in gwamnatin yankin musammam na HK na kasar Sin, ya yi kira da a zauna lafiya don ci gaba da rike masu basira a yankin.

Babban sakataren gudanarwa, Matthew Cheung, ya bukaci a gaggauta dawo da zaman lafiya yankin HK domin al'ummomin kasashen duniya su kara amincewa da kwarin gwiwa kan yankin, da darajarsa a idon duniya.

Cikin mukalar da yake wallafawa a kowane mako, Matthew Cheung ya ce ba makawa wasu masu basira na yankin da ma na kasashen waje, na duba yuwar raya ayyukansu a wasu wurare saboda dalilai daban daban, la'akari da yanayin da ake ciki.

Sai dai, Cheung ya jaddada cewa, yankin bai yi wata gagagrumar asarar masu basira, wadanda fa'idoji da gogayyarsu suka yi fice tsakanin hukumomin kasa da kasa ba.

Babban jami'in ya kara da cewa, jan hankalin masu basira na da muhimmanci ga ci gaban HK, wanda ke fuskantar kalubalen karancin ma'aikata da yawan wadanda suka manyanta.

Ya ce gwamnatin yankin, za ta ci gaba da aiki kan tsarin albarkar jama'a, domin HK ta kara zama abun gogayya da kuma taimakawa matasa samun damar cin gajiyar ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China