Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka
2019-12-02 17:48:12        cri
A game da yadda Amurka ta kare aniyarta ta sanya hannu kan shirin doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong a kwanakin baya, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin madam Hua Chunying ta sanar a yau Litinin cewa, Sin za ta kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka don mayar da martani.

Madam Hua ta ce, abun da Amurka ta yi ya sabawa dokoki gami da ka'idojin kasa da kasa, wanda kuma ya zama shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin. A don haka, gwamnatin Sin ta yanke shawarar daukar matakan sanyawa Amurka takunkumi, inda tun daga yau ranar 2 ga wata, Sin za ta dakatar da duba rokon da jiragen yakin sojan Amurka suke gabatarwa na samun hutu a Hong Kong, da garkama takunkumi kan wasu kungiyoyin Amurka da ba na gwamnati ba wadanda suka aikata munanan laifuka a rikicin Hong Kong, ciki hadda kungiyoyin NED da NDI da IRI da HRW da Freedom House da sauransu.

Madam Hua ta jaddada cewa, Sin ta bukaci Amurka ta gyara kuskuren da ta aikata, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar. Har wa yau, Sin za ta yi la'akari da halin da ake ciki don kara daukar matakan da suka wajaba na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankin Hong Kong, da kare ikon kasar da tsaro gami da ci gabanta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China