Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muryar GBA: Jefa kuri'a don kwantar da tarzoma a Hong Kong
2019-11-24 15:57:21        cri

Rediyon muryar babban yankin bakin teku na Guangdong da Hong Kong da Macao (GBA) karkashin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya watsa wani shari a jiya Asabar, inda aka yi kira ga jama'ar yankin musamman na Hong Kong da su jefa kuri'unsu a zaben majalissun yankuna daban daban na Hong Kong, da zai gudana a yau Lahadi, don kar a bata wani zarafi mai muhimmanci na jefa kuri'a don ganin bayan karfin tuwo, da kuma sanya Hong Kong ya fito daga mawuyacin halin da yake fuskanta.

A cikin sharhin, an ce, idan an waiwaya abubuwan da suka faru cikin watanni 5 da suka wuce, za a ga yadda wasu 'yan majalissun wurin masu dauke da ra'ayi na adawa suka yi kokarin ta da rikici a yankin. Inda suka nuna goyon baya ga 'yan tarzoma, ta yadda aka yi kokarin tsokana 'yan sanda, da neman ganin lalacewar muhallin yankin. Saboda haka, dole ne a samu sabbin 'yan majalissu a yankin, wadanda za su yi kokarin bautawa jama'a, da sauke nauyin dake bisa wuyansu na tabbatar da makomar yankin Hong kong, don maye gurbin wadanda ke neman ta da rikici a Hong Kong.

An jaddada a cikin sharhin cewa, a yau Lahadi an samu damar kubutar da yankin Hong Kong ta hanyar jefa kuri'a, don haka ya kamata a yi amfani da wannan dama da kyau, don tabbatar da makomar yankin mai haske. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China