Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin HK ta yi bakin ciki sosai kan matakin majalisar dattawan Amurka
2019-11-21 11:04:23        cri

Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ta nuna bakin ciki sosai kan yadda a ranar 20 ga wata majalisar dattawan kasar Amurka ta zartas da shirin doka game da yadda ake kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya a yankin Hong Kong na shekarar 2019.

Kakakin gwamnatin Hong Kong ya yi nuni da cewa, abin da majalisar dattawan Amurka ta yi ba mataki ne da ya wajaba ba, kuma ba shi da wani dalili, ban da haifar da illa ga huldar da ke tsakanin yankin Hong Kong da Amurka da kuma muraddunsu. Bai kamata ba majalisar wata kasa ta tsoma baki a harkokin cikin gida na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ta duk wata hanya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China