Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon kyaftin din Najeriya ya yaba kwazon Super Eagles
2019-11-21 10:59:33        cri
Tsohon kyaftin din tawagar 'yan kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles Segun Odegbami, ya yaba nasarar da 'yan wasan suka samu kan takwarorinsu na kasar Lesotho,(Crocodiles of Lesotho) a wasan farko da suka buga na neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2021.

Odegbam, wanda ya bayyana haka yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce, nasarar da 'yan wasan suka samu, za ta kara musu kwarin gwiwa.

Nasarar da Najeriya ta samu da ci 4 da biyu a Masesu a ranar Lahadin da ta gabata, ya sanya ta zama jagorar rukuni na 12 wato (L )na gasar ta AFCON, da maki 6. A shekara mai kamawa ne, za ta kara da kasar Saliyo.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China