Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya ta lashi takwabin karfafa yin takara a kasuwar hannajen jarin kasar
2019-11-22 11:08:16        cri

Gwamnatin Najeriya ta ba da tabbacin cewa, za ta bullo da wasu managartan matakai a bangaren harkokin kudin kasar, da ma samar da yanayin da ya dace na karfafa yin takara a kasuwar hannayen jarin kasar.

Ministan masana'antu, cinikayya da zuba jari na kasar Niyi Adenayo ne ya bayyana hakan, yayin taron shekara-shekara na manyan cibiyoyin kula da harkokin zuba jari da ya gudana a jihar Lagos dake yankin kudu maso yammacin kasar. Ya ce, manufar shirin, ita ce tabbatar da raya tsarin tattalin arziki mai karfi, musamman bisa la'akari da bangaren kudi.

Ministan ya ce, hanya mafi kyau ta inganta yin takara, ita ce hade manufofi da aka tsara, ta yadda za a inganta yin takara a kasuwar hannayen jari da ma yadda za a zuba jari na dogon lokaci, ana kuma fatan matakan za su inganta takara a bangaren farashi da ma wanda bai shafi farashi ba.

Ya ce, galibin tsare-tsaren harkokin kudi a sassan duniya, suna da matukar tasiri kan ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci. Don haka, a cewar minista Adebayo, akwai bukatar a daidaita yanayin dake shafar harkokin kasuwanci, ta yadda za a samar da yanayin zuba jari da ya dace, wanda gwamnatin Najeriya za ta goyi baya a ko wane lokaci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China