Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace wani babban jami'inta a jihar Adamawa
2019-11-21 11:04:42        cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta tabbatar a Jiya Labara cewa, wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da babban jami'inta mai kula da yankin Mubi dake jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin kasar Mai suna Ahijo Mujeli, ranar Talata da dare yayin da yake tuka motarsa.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa Suleiman Yahaya, ya bayyana cewa, an ji karar harbin bindiga mai karar gaske a kusa da hanyar Mubi-Maraba dake yankin Mubi ta arewa a jihar ta Adamawa, inda aka yi awon gaba da jami'in dan sandan.

Sai dai, lokacin da 'yan sanda suka isa wurin, babu kowa a cikin motar jami'in da aka sace.

Kakakin 'yan sandan ya ce, an kaddamar da bincike don gano inda babban jami'in dan sandan da aka sace.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China