2019-12-06 10:26:34 cri |
Jakada Liao, ya shaidawa taron manema labarai da aka shirya a ofishin jakadancin Sin dake birnin Alkahira cewa, a 'yan shekarun nan, an samu ci gaba sosai a hadin gwiwar dake tsakanin Masar da Sin bisa manyan tsare-tsare. A mataki na siyasa, a shekarar da ta gabata, manyan jami'an sassan biyu sun ziyarci juna a lokuta daban-daban.
Ya ce, a shekarar 2019 da muke ciki, kusan tawagogin kasar Sin 30 ne suka ziyarci kasar Masar, yayin da ita kuma kasar Masar ta aika tawagogi 20 zuwa kasar Sin. Wadannan ziyarce-ziyarce tsakanin sassan biyu, sun shafi fannonin cinikayya da aikin gona da fasahar kere-kere da binciken kayayyakin tarihi.
Liao ya kara da cewa, a 'yan shekarun nan, alakar Sin da Masar a fannin cinikayya da tattalin arziki ta bunkasa matuka, inda ya ba da misali da yankin masana'antu na TEDA da aikin gina babban yankin kasuwanci dake tsakiyar sabon birnin Masar, a matsayin misali na kyakkyawar alakar dake tsakanin sassan biyu. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China