Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Sin sun shiga bikin baje kolin fasahohin zamani a Masar
2019-12-02 10:15:32        cri

Kamfanonin kasar Sin sun shiga gagarumin bikin baje kolin fasahar sadarwa ta zamani wato (ICT) wanda aka fara daga ranar Lahadi za birnin Alkahira na kasar Masar wanda ya samu halartar kamfanonin kasashen waje da na cikin gidan kasar kusan 500.

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, shi ne ya kaddamar da bikin baje kolin na fasahohin zamani karo na 23 wato Cairo ICT 2019, taken bikin na bana shi ne "musayar kwarewar zamani" a daidai lokacin da kasar Masar ke kokarin tabbatar da sauye-sauyen zamani ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin fasahohin zamani na kasa da kasa.

Daga cikin kamfanonin kasar Sin da suka baje hajarsu, akwai cibiyar nazarin na'urori masu sarrafa kansu ta Jiangsu wato (JARI) a takaice, wacce ta kware wajen samar da tsarin samar da bayanan sirri da na'urorin zamani masu ruwa da tsaki. JARI, wani bangare ne na babban kamfanin fasahar zamani na CSBC na kasar Sin, ya shiga baje kolin Cairo ICT 2019 inda ya nuna wasu mutum-mutumi nau'i daban daban.

Fan Jun, janar manajan sashen ciniki na kasa da kasa na kamfanin JARI, ya ce za'a iya yin amfani da mutum-mutumin wajen binciken dan Adam, da aikin ceto daga bala'u, da kuma aikin kashe gobara.

Janar manajan ya ce, halartar bikin baje kolin da kamfanin na JARI ya yi wani bangare ne na shawarar "ziri daya da hanya daya" (BRI), wanda kasar Sin ta gabatar da ita, da nufin neman ci gaba ta hanyar cin moriyar juna a tsakanin kasashen dake cikin shawarar BRI ciki har da kasar Masar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China