![]() |
|
2019-12-19 20:08:14 cri |
Shugaba Xi wanda ya samu rakiyar jami'in farko na gudanarwar yankin na Macao Chui Sai On, yayin ziyarar cibiyoyin gwamnati dake yankin Areia Preta, da makaratar "Premier" dake karkashin makarantar midil ta Hou Kong, ya yaba da salon kishin kasa a tsarin ilimin Macao, yana mai kira da a kara azama a wannan fanni.
Xi Jinping ya ce salon ilimi mai kunshe da kishin kasa, shi ne ginshikin managarcin tsarin zamantakewa da siyasa a Macao, wanda kuma yake ingiza aiwatar da salon jagoranci na 'kasa daya, tsarin mulki biyu', ya kuma dora yankin kan turba ta gari.
Yayin ziyararsa a yankin na Macao, shugaba Xi ya kuma yi rangadi a cibiyar habaka cinikayya da kasuwanci ta kasashen dake magana da yarukan Sinanci da Portuguese da ke yankin.
Shugaba Xi ya isa yankin Macao ne, domin halartar bikin cikar shekaru 20 da komowar yankin hannun babban yankin kasar Sin. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China