Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: "Kasa daya, tsarin mulki biyu" ya amfani yankin Macao sosai
2019-12-19 21:29:58        cri

Daren yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin liyafar maraba da zuwansa da gwamnatin yankin Macao ta shirya, tare da ba da jawabi. Inda Shugaba Xi Jinping ya ce, a cikin shekaru 20 da suka gabata, tun bayan dawowar yankin hannun babban yankin kasar Sin, yankin Macao ya samu bunkasuwa mafi sauri, da samun kyautatuwar zaman rayuwar jama'a mafi kyau, kuma jama'ar yankin na ganin yadda suke cin moriya, dangane da mutunci da alfaharin kasarsu.

Ya ce bunkasuwa da kuma juyin juya hali da yankin ke fuskanta, na dogaro da tsarin "kasa daya, tsarin mulki biyu", kuma hakan na da alaka sosai da goyon bayan da gwamnatin tsakiya, da babban yankin ke nuna masa, kana yana da nasaba da matakan da gwamnatin yankin ke dauka, da kokarin da al'umomin yanki suke yi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China