Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kuduri aniyyar taimakawa ayyukan bincike da kirkire-kirkire da matasa masana za su gudanar
2019-09-04 10:11:27        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana kudurin kasarsa, na ganin an samarwa matasa masana goyon baya da yanayin da ya dace na gudanar da bincike da kirkiro sabbin abubuwa.

Ya ce, gidauniyar kimiyya ta kasa da aka tanada don matasa masana kimiyya, za ta taka muhimmiyar rawa, wajen taimakawa masu bincike da kudaden da ake bukata a aikin bincike da kirkire-kirkire.

Li ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi a taron dandalin aikin kafa asusun, wanda aka gudanar ranar Litinin din da ta gabata. Ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ta kara karfafa yin bincike, a kokarin kafa wani harsashe mai karfi ga shirin raya kirkire-kirkire na kasar Sin.

Jami'in na kasar Sin ya kuma ba da shawarar amfani da asusun, a matsayin "asusun zuba jari", inda za a rika bunkasa harkokin kirkire-kirkire, ta yadda za a rika karfafawa karin masana kimiyya da fasahar kere-kere, musamman matasa masu hazaka gwiwar zakulo sabbin abubuwa a fagage daban-daban.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China