Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin Firaministan kasar Sin ya jaddada muhimmancin inganta ci gaban fasahar zamani
2019-08-27 11:22:18        cri
Mataimakin Firaministan Sin Liu He, ya yi kira da a yi amfani da sababbin damarmaki dake akwai a fannin ci gaban fasaha, domin inganta ci gaban masana'antar fasahar zamani.

Liu He wanda kuma mamba ne na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana haka ne yayin bude taron baje kolin kayayyakin fasaha na 2019 na kasar Sin, jiya Litinin a birnin Chongqing.

Yayin bikin bude taron, mataimakin Firaministan ya kuma karanta wasikar taya murna da shugaba Xi Jinping na kasar, ya aike ga taron.

Wasikar ta yi cikakken bayani kan yadda shugaban ke bada muhimmanci ga raya fasahar zamani da kuma bayyana alkiblar samar da ci gaban bangaren.

Liu He ya kuma bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na sauyawa daga mai tafiya cikin sauri zuwa mai inganci sosai. Yana mai cewa gamsassun manufofin tattalin arziki da sauye-sauyen bangarorin dake ba da gudummawa ga tattalin arzikin, za su iya tabbatar da ingancin tubalin tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China