Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#MacaoSAR 20#Xi Jinping: Tsayawa ga manufar "kasa daya da tsarin mulkin biyu" shi ne dalilin da ya sa Macao ya samu nasara
2019-12-20 11:03:20        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Jumma'a cewa, ci gaba da nasarorin da yankin Macao ya samu bayan dawowarsa babban yankin kasar Sin, sun shaida cewa, muddin aka nuna imani ga manufar "kasa daya tare da tsarin mulkin biyu",hakika, za ta kara taka rawar a-zo-a-gani.

Xi ya ce, gwamnati gami da bangarori daban-daban na yankin Macao suna tsayawa tsayin daka wajen kare 'yancin kasar Sin da tabbatar da tsaro da ci gaba da kuma muradunta, a yayin da suke kokarin kiyaye bunkasuwa da kwanciyar hankali a yankin Macao. Haka kuma suna more irin damammakin da manyan tsare-tsare gami da manufofin ci gaba da kasarsu ta Sin ta samar, inda suke neman ci gaban kansu da na kasa baki daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China