Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#MacaoSAR 20#Yankin Macao ya samu kyakyyawar bunkasuwa, in ji Xi Jinping
2019-12-20 10:58:23        cri
A jawabin da ya gabatar yau, yayin bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Macao karkashin ikon kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya nuna yabo matuka kan babbar bunkasuwar da yankin Macao ya samu cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, lamarin da ya sa, yankin ya shiga yanayi mafi kyau cikin tarihinsa.

Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 20 da suka gabata, an ci gaba da kyautata tsarin tafiyar da harkokin yankin, bisa tsarin mulkin kasar Sin da babbar dokar yankin Macao. Yankin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan kwamitin tsakiyar kasar Sin game da tafiyar da harkokin Macao bisa dukkan fannoni, kuma yankin Macao yana da 'yancin tafiyar da harkokinsu bisa doka yadda ya kamata. Ana kuma kiyaye 'yancin al'ummomin yankin bisa dokokin kasa. Bugu da kari, tattalin arzikin yankin ya samu babban ci gaba, zaman rayuwar al'ummomin yankin na ci gaba da samun kyautatuwa, lamarin da ya sa, yankin ya zama daya daga cikin birane mafiya tsaro a duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China