Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#MacaoSAR 20#Xi Jinping: ko da yaushe Macao na bin manufar "Kasa daya amma tsarin mulki biyu" yadda ya kamata
2019-12-20 10:54:13        cri
Yau a gun babban taron cika shekaru 20 da dawowar yankin musamman na Macao karkashin ikon kasar Sin, gami da bikin rantsar da shugabannin gwamnatin yankin karo na 5, shugaban kasar Xi Jinping ya nuna cewa, an samu gagarumar nasara a Macao tun bayan dawowarsa karkashin ikon kasar Sin ne sakamakon kyakkyawar manufar da yake bi ta "Kasa daya amma tsarin mulki biyu". Mazauna yankin sun amince da cewa, "kasa daya" shi ne tushen "tsarin mulki biyu".

Bugu da kari, hukumomin harkokin siyasa da kafa doka da na shari'a na yankin su ma suna bin manufar "kasa daya", da kiyaye ikon gwamnatin tsakiya na kasar da martaban babbar doka ta yankin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China