Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya bayyana alfahari da ci gaban Macao
2019-12-18 19:19:46        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce gwamnatin babban yankin kasar Sin na alfahari da irin gagarumin ci gaba da yankin Macao ya samu cikin shekaru 20 da suka gabata.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban kwamitin kolin rundunar sojojin kasar, ya yi wannan tsokaci ne bayan da ya sauka a yankin Macao da yammacin yau Laraba. Yayin da yake tsokaci ga manema labarai a filin jirgin saman yankin, shugaba Xi ya ce "Na yi farin cikin sake zuwa Macao. A watan Oktoba, mun gudanar da babban bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Wannan biki na murnar cika shekaru 20 da sake dawowar yankin Macao babban yankin Sin wani babban al'amari ne a tarihi,".

Shugaban na Sin ya kuma gabatar da sakon taya murna da fatan alheri ga al'ummar yankin Macao game da wannan biki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China