Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya isa yankin Macao
2019-12-18 16:57:48        cri

 

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin koli na soja, Xi Jinping ya isa yankin Macao a yammacin yau Laraba, don halartar bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin cikin hannun babban yanki.

An ba da labari cewa, ran 20 ga watan Disamba na shekarar 1999, gwamnatin kasar Sin ta maido da ikon mulkinta kan yankin Macao, hakan ya sa, yankin ya dawowa hannun babban yankin. A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, ci gaban da aka samu wajen aiwatar da manufar "kasa daya tsarin mulki" a yankin ya amfanawa bunkasuwar yankin dake gabar tekun kudu na kasar Sin cikin sauri. Yawan GDPn yankin ya karu zuwa Pataca biliyan 444.7 na shekarar 2018 daga Pataca biliyan 51.9 na shekarar 1999, matsakaicin GDP na kowane mutum na sahun gaba a duniya, ban da wannan kuma, yawan rashin aikin yi ya ragu zuwa kashi 1.8 cikin dari na shekarar 2018 daga kashi 6.3 cikin dari na shekarar 1999.

Daga ran 18 zuwa 20 ga wata, shugaba Xi Jinping zai halarci babban taron murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin cikin hannun babban yankin kasar Sin, da bikin rantsuwar kama aiki na gwamnatin yankin karo na 5, tare da kai rangadi a yankin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China