Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya halarci bikin kaddamar da jirgin dakon jirage kirar Sin na farko
2019-12-17 19:35:31        cri
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar ta Sin Xi Jinping, ya halarci bikin kaddamar da jirgin dakon jirage na farko da aka kera a kasar Sin.

An dai gudanar da bikin kaddamar da jirgin da aka sawa suna Shandong ne da yammacin Talatar nan, ya kuma ci sunan lardin Shandong dake gabashin kasar Sin inda aka kaddamar da shi.

Bayan kaddamar da jirgin, an mika shi ga rundunar 'yantar da al'umma ta sojin ruwan kasar inda zai fara aiki a tashar Sanya, dake lardin Hainan na kudancin kasar ta Sin. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China