Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bada tabbacin mayar da martani game da shingen da Amurka ta sanyawa jami'an diflomasiyyarta
2019-12-07 16:45:34        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, game da matakin da kasar Amurka ta dauka a watan Oktobar bana na kafa shinge kan jamai'an diplomasiyyar kasar Sin dake Amurka, kasar Sin ta riga ta kirawo ofishin jakadancin kasar Amurka dake Sin a ranar 4 ga wata, cewa daga wannan rana kasar Sin ta dauki mataki makamancin wanda Amurka ta dauka.

Hua ta bayyana haka ne a yayin taron menma labaru da aka shirya a jiya Jumma'a, inda ta kara da cewa, ko da yaushe kasar Sin na goyon bayan duk wani jami'in diplomasiyya daga kasashen ketare dake nan kasar Sin, ciki har da na kasar Amurka, don su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tana kuma samar musu da saukin da ya wajaba. Game da matakin kafa shinge da kasar Amurka ta dauka kan jami'an diplomasiyyar kasar Sin dake Amurka, Sin ta riga ta dauki irin mataki kan jami'an diplomasiyyar Amurka, nan gaba kuma zata mayar da martani bisa matakan da Amurkar zata dauka. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China