Ya kamata a rage harajin kwastam idan Sin da Amurka suka cimma yarjejeniya a mataki na farko
Ci gaban shawarwarin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka ya fi jan hankalin kasa da kasa. Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, a ganin kasar Sin, idan kasashen biyu suka cimma yarjejeniya a mataki na farko, ya kamata a rage harajin kwastam da abin ya shafa. Tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu na tuntubar juna game da wannan batu. (Zainab)
Labarai masu Nasaba