Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta bullo da tsarin auna hidimar da gwamnati ke samarwa jama'a
2019-12-18 12:11:27        cri

Babban ofishin kula da harkokin majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar tana shirin bullo da wani tsarin da jama'a da kamfanoni, za su rika auna ingancin hidimar da gwamnati take samarwa.

Manufar tsarin wanda ake saran zai fara aiki gadan-gadan ya zuwa karshen shekarar 2020 ita ce, inganta sha'anin tafiyar da harkokin mulki da kara fadakar da jama'a game da abubuwan da suka shafi hidimomin da gwamnatoci ke samarwa a dukkan matakai.

Bisa tsarin, kamfanoni da jama'a, za su auna ingancin hidimomin da gwamnati take samarwa a inda suke ko ta yanar gizo, ta hanyar akwatuna gabatar da koke-koke da layukan musamman da za a samar. Za a sanar da jama'a wadannan sakamako, tare da sanya su cikin rahoton auna kwazon gwamnati. Haka kuma, ka'idojin ya bayyana cewa, ya kamata a bullo da matakan daidaita binciken sakamakon alkaluma marasa kyau da koke-koke da aka samu yayin gudanar da wannan shiri.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China