Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron karawa juna sani kan "Sin da duniya a sabon zamani"
2019-12-17 13:56:30        cri

An yi wani taron sanin makamar aiki na kasa da kasa mai taken "Sin da duniya a sabon zamanin da muke ciki" jiya Litinin a birnin Beijing, inda mahalarta taron suka nuna cewa, yayin da duniya ke kara fuskantar kalubaloli daban-daban, bai kamata a raba ci gaban kasar Sin da duniya ba, sannan ya kamata kasashen duniya su saurari ra'ayin kasar. Sin babbar kasa ce dake daukar babban nauyi, wadda ke bayar da muhimmiyar gudummawa a fannonin shimfida zaman lafiya da neman ci gaba tare a duniya yayin da take raya kanta.

Taron ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnati da jakadun kasashen waje dake kasar Sin da kwararru da masana gami da wakilai daga kamfanoni daban-daban na kasashen Poland da Portugal da Kirghizstan da Masar, inda suka tattauna kan batutuwan da suka jibanci ci gaban da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta samu a cikin shekaru saba'in, da babbar ma'anar ci gaban kasar ga duniya, da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, tare kuma da yadda za'a tafiyar da harkokin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China