Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira da a magance matsalar 'yan gudun hijira daga tushe
2019-12-18 10:03:02        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya jaddada bukatar magance matsalar 'yan gudun hijira daga tushe, ta yadda za a inganta matakan da kasashen duniya ke dauka game da halin da 'yan gudun hijirar ke ciki.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai da aka shirya a taron dandalin 'yan gudun hijira na duniya dake gudana a halin yanzu. Yana mai cewa, yanzu ne za a tabbatar da cewa, an kare 'yancin 'yan gudun hijira, da sake dawo da martabar tsarin kare martabar 'yan gudun hijira na kasa da kasa, aka kuma fara magance dalilan dake sanya mutane barin garuruwansu.

Haka kuma, jami'in na MDD ya bayyana cewa, duniya tana bukatar a canja hanyar da ake bi wajen kula da halin 'yan gudun hijira ke ciki, ta yadda za a tunkuri matsalolin da ake ciki a halin yanzu da ma shiryawa kalubalen dake gaba.

Alkaluma na baya-bayan da MDD ta fitar sun nuna cewa, an tilastawa mutane sama da miliyan 70 barin muhallansu, adadin da ya ninka na shekaru 20 da suka gabata har sau biyu.

Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD (UNHCR) da gwamnatin Switzerland tare da hadin gwiwar kasashen Costa-Rica da Habasha da Jamus da Pakistan da Turkiya ne, suka shirya taron dandanlin 'yan gudun hijira na duniya na kwanaki uku a birnin Geneva da aka bude ranar Litinin da ta gabata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China