Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen kudu da hamadar Sahara sun sha alwashin baiwa yan gudun hijira damar kada kuriu
2019-11-29 10:07:38        cri

Jagororin kasashen dake kudu da hamadar Saharar Afirka, sun sha alwashin samar da dokoki da tsare tsare, wadanda za su baiwa al'ummun yankin dake gudun hijira a ciki da wajen kasashen su, damar kada kuri'u yayin gudanar da zabubbuka.

Shugabannin sun tabbatar da wannan aniya tasu ne, yayin taron nahiyar Afirka na 6 game da harkokin zabe, wanda kasar Kenya ta karbi bakunci. Taken taron shi ne "inganta shigar 'yan gudun hijira, da wadanda suka kauracewa gidajen su damar shiga zabuka a Afirka".

Cikin jawabin sa a taron na jiya Alhamis, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, wanda babban mai shari'ar Kenya Paul Kihara ya karanta, ya ce 'yan gudun hijirar Afirka da dama na samun mafaka a wajen nahiyar, yayin da wasu ke fakewa a cikin kasashen su, wannan rukuni na mutane na fuskantar manyan kalubale, don haka akwai bukatar shigar da su cikin tsarin zabukan nahiyar, ta yadda za su samu wakilci.

Manyan jami'ai masu tsara manufofi, da kwararru a fannoni daban daban sun halarci wannan taro, inda da dama suka jaddada muhimmancin tabbatar da hakkokin 'yan gudun hijira da tashe tashen hankula suka raba da muhallansu, da wadanda annoba ta kora, matakin da a cewar su zai tabbatar da nasarar bunkasuwa, da daidaito, da ma zaman jituwa tsakanin al'ummun nahiyar ta Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China