Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan Borno ya baiwa 'yan Najeriya dake gudun hijira a Kamaru tabbacin komawa gida lafiya
2019-09-19 10:15:22        cri
Gwamnan jihar Borno a tarayyar Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya baiwa'Yan gudun hijirar Najeriya dake zaune a sansanin Minawao dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru tabbacin komawa gida lami lafiya ba tare da wani bata lokaci ba.

Gwamna Umara ya bayyana haka ne, a zantawarsa da manema labarai yayin ziyarar da ya kai sansanin 'yan gudun hijira mafi girma na Minawao dake kasar Kamaru. Ya ce, yana son 'yan gudun hijirar su dawo gida, ya kuma shaida masu irin kyawawan tanade-tanaden da gwamnatin tarayya da ta jihar Borno suke da shi, cewa za su yi duk mai yiwuwa na ganin sun dawo gida cikin mutunci.

Ya kuma yaba da kokarin da gwamnatin Kamaru da kungiyoyin jin kai na kasa da kasa suke yi na tabbatar da kula da lafiyar 'yan gudun hijirar dake sansanin na Minawao.

A watan da ya gabata ne dai, aka kwashe rukunin farko na 'yan gudun hijira 133 daga sansanin zuwa Najeriya.

'Yan gudun hijirar dai sun arcewa hare-haren mayakan Boko Haram ne, inda suka samu mafaka a sansanin na Minawao da yanzu ke dauke da sama da 'yan gudun hijirar Najeriya 57,000.

Shi dai yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru ya hada iyaka ne da jihar Borno.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China