Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: 'Yan gudun hijira miliyan 10.5 ne suka samu kulawar kiwon lafiya a shekarar 2018
2019-07-19 10:06:12        cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana cewa, kimanin 'yan gudun hijira miliyan 10.5 ne suka samu kulawar kiwon lafiya ta hanyar shirye-shiryen samar da lafiya ga jama'a na hukumar a shekarar da ta gabata, duk da adadi mafi yawa na mutanen da aka raba da muhallansu a duniya da yadda har yanzu matsalar 'yan gudun hijira ke ci gaba da karuwa.

Hukumar ta bayyana cikin wani rahoton shekara-shekara dake nazarin kiwon lafiyar al'umma na duniya cewa, ita da abokan huldarta ne suka wallafa wadannan alkaluma a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya nuna cewa, ci gaban da aka samu a shekarar 2018 da ta gabata, yawan mace-mace tsakanin yara 'yan gudun hijira 'yan kasa da shekaru biyar, wani abu mai muhimmanci a bangaren lafiya ya ci gaba da raguwa. Bugu da kari, rahoton ya bayyana muhimmin ci gaba da aka samu wajen sanya 'yan gudun hijira cikin tsare-tsaren kiwon lafiya na kasa.

Rahoton ya ce, wasu kasashe na kokari matuka wajen fadada damammakin sanya 'yan gudun hijira cikin shirye-shiryen inshorar kiwon lafiya da sauran matakan ba da kariya ga ginshikan rayuwa.

Yanzu haka, galibin 'yan hijira a kasashe 37 da suke samun mafaka, suna samun allurar riga kafi da magungunan tarin fuka, da na kanjamau da zazzabin cizon sauro daidai da 'yan kasashen.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China