Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude dandalin tattauna batun 'yan gudun hijira a Geneva
2019-12-17 15:11:05        cri
An kaddamar da wani dandalin tattaunawa na kasa da kasa kan batun 'yan gudun hijira karo na farko a birnin Genevan kasar Switzerland jiya Litinin.

Dandalin, wanda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin kasar Switzerland suka dauki nauyin shiryawa zai maida hankali kan bullo da wani shiri na dogon lokaci don taimakawa 'yan gudun hijira daga kasashe daban-daban gami da kasashe da unguwannin da suka karbe su.

Wasu manyan kasashe biyar da suka karbi 'yan gudun hijira sun taimaka wajen gudanar da wannan dandalin na tsawon yini uku, ciki hadda Costa Rica da Habasha da Jamus da Pakistan da kuma Turkiyya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China