Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR: Sama da yan gudun hijira miliyan 1.44 za su bukaci a sake tsugunar da su a shekarar 2020
2019-07-02 10:13:07        cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta yi kiyasin cewa, a shekarar 2020 dake tafe, sama da 'yan gudun hijira miliyan 1.44 da a halin yanzu ke zaune a sama da kasashe 60 da suka tsugunar da 'yan gudun hijira, za su bukaci a sake tsugunar da su .

Babban kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya bayyana hakan, ya ce, bisa la'akari da adadin mutanen dake neman tsira daga yaki, tashin hankali da hukunci da rashin matakai na siyasa kan wadannan yanayi, akwai bukatar kasashe su tsara matakan sake tsugunar da karin 'yan gudun hijira.

Jami'in na MDD ya ce, ya bude taron tuntuba na kwanaki biyu tsakanin sassan uku game da sake tsugunar da 'yan gudun hijira (ATCR) na shekara-shekara a birnin Geneva.

Wani rahoto kan hasashen bukatar sake tsugunar da 'yan gudun hijira na duniya a shekarar 2020, da aka kaddamar a taron na ATCR, ya nuna cewa, kashi 40 cikin 100 na 'yan gudun hijirar Syria na cikin hadari kuma suna bukatar sake tsugunar da su. Sai kashi 14 cikin 100 na 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu, yayin da kaso 11 cikin 100 na 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ke cikin wannan hali.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China