![]() |
|
2019-12-15 16:45:42 cri |
Da yake jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa tare da mataimakin firaministan Slovenian kana ministan harkokin wajen kasar, Miro Cerar, Wang Yi ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da CEEC, wadda aka fi sani da hadin gwiwar 17+1, wata muhimmiyar hadin gwiwa ce da ta ratsa shiyyoyi bisa tushen muradun bangarorin Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai, kuma ta riga ta samar da kyakkyawan sakamako a kan lokaci, kana muhimmin sakamakon da aka samu karkashin hadin gwiwar ya shafi fannoni kusan 20.
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron kolin 17+1 a watanni shidan farko na shekarar 2020, Wang ya ce, wannan ya kara nuna yadda hadin gwiwar ta baiwa kasar Sin muhimmanci mai girma, kuma Sin tana ci gaba da mutunta bukatu da moriyar kasashen na Turai 17, da nufin kara zurfafa matsayin hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu.
Karkashin taron kolin, kasar Sin tana fatan daga matsayin hadin gwiwar karkashin manufar cin moriyar kowane bangare, da sake bude sabbin damammakin cin moriyar juna ga dukkan bangarorin, kana da kara ingiza ci gaban dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China