Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron sauyin yanayi na MDD
2019-12-16 10:43:27        cri

A jiya ne aka kammala taron sauyin yanayi na MDD (COP25), bayan lokacin da aka kara na zaman taron, yayin da masu mahalarta taron suka kasa cimma matsaya kan aya ta 6 ta yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015 game da matakan da kasashe za su dauka wajen rage fitar da hayaki mai gurba muhalli.

A baya dai an shirya kasashen za su cimma daidaito ne a ranar Jumma'a, amma sai aka ci gaba da taron har zuwa ranar Asabar da kuma Lahadi da safe. Inda aka kara sama da sa'o'i 40, abin da ya sa taron na bana zama taron sauyin yanayi mafi tsawo a tarihi, ba kamar yadda aka saba ba, bayan da aka kara lokaci saboda rashin cimma matsaya.

Yayin rufe taron, wakilai daga galibin kasashe sun bayyana bacin ransu, saboda gaza cimma yarjejeniya kan aya ta 6. Hakan na nufin za a kara tattaunawa a kan wannan batu a taron da za a yi badi a Glasgow.

A jawabin da ya gabatar a madadin kasashen Sin da Brazil da Indiya da Afirka ta kudu yayin rufe taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron, kana mataimakin ministan yanayi da muhallin halittu Zhao Yingmin, ya ce, "Sakamakon taron bai kai ga yadda muka yi zato ba, musamman babban batun da aka tattaunawa, game da za a aiwatar da aya ta 6 wadda ba a warware ta ba. Na yi imanin cewa, dukkan mu ba mu ji dadi ba, sannan ra'ayin mu sun sha bamban."

Zhao, ya kuma bayyana cewa, kasashen Sin da Brazil da Indiya da Afirka ta kudu ba su ji dadin yadda kasashen da suka ci gaba ba su amsa bukatun kasashe masu tasowa na samar musu da kudade ba. Haka kuma kasashen hudu, sun bayyana takaicinsu kan damar da kasashe ta aiwatar da matakan da suka tsara game da fitar da hayaki mai gurbata muhalli a shekarar 2020.

Don haka ya bukaci kasashen da suka ci gaba, da su dauki managartan matakai na cike gibin rage hayaki mai illa ga muhalli da ma taimakawa kasashe masu tasowa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China