Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Fadan kabilanci babban kalubale ne ga yammacin Afirka
2019-12-17 09:43:25        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana fadan kabilanci a matsayin babban kalubale dake addabar yammacin Afirka, da ma yadda karuwarsa ke da alaka da ta'addanci.

Zhang Jun ya bayyana haka ne, yayin zaman kwamitin sulhun MDD game da yammacin Afirka, yana mai cewa, matsalar tana shafar shiyyar baki daya. Ya kuma bayyana cewa, kaurar jama'a tana kara gasar mallakar albarkatu kamar filaye da ruwa, lamarin da ke haddasa yawaitar tashin hankali tsakanin manoma da Fulani makiyaya.

Bugu da kari, bambancin kabila da addini, da matsalar sauyin yanayi da yaduwar makamai da sauran dalilai sun kara ta'azzara matsalolin.

Ya ce, abin damuwa shi ne, a 'yan shekarun nan, ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi sun yi amfani da wadannan matsaloli. Ya kuma buga misali cewa, Boko Haram da IS sun ci gaba da girma a yammacin Afirka, kana 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayi sun sake dawowa, inda suka rika amfani da tashin hankali wajen kaddamar da hare-hare, hakan ya haifar da barazanar zaman lafiya da tsaro a shiyyar baki daya.

A don haka, ya ba da shawarar cewa, ya kamata a raya tattalin arziki da jin dadin jama'a, ta hanyar kara zuba jari da cinikayya a nahiyar Afirka, ta yadda za a kawar da talauci.

Ya kara da dewa, ya kamata a samar da damammaki a fannonin ilimi da aikin yi, musamman ga matasa, haka kuma ya dace a ba da 'yancin bunkasa al'ummomin daban-daban ta hanyar samar da hidimmomi ga jama'a daidai wa daida.

Wakilin na kasar Sin, ya kuma bayyana cewa, kasarsa tana taimakawa kasashen dake shiyyar da kayayyakin more rayuwa, a wani mataki na kara karfin hanyoyin nahiyar, da ilimi da damammaki na koyon sana'o'i ga matasan nahiyar, ta hanyar ba su guraben karo ilimi a kasar Sin, da kafa cibiyoyin ilimi da samun horo da sauransu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China