Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummomin Sinawa biliyan 1.4 na fatan a hanzarta kwantar da kura a yankin Hongkong
2019-08-22 20:26:18        cri
A yau Alhamis, a yayin wani taron manema labaru da aka shirya, Mr. Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, babban burin al'ummomin Sinawa biliyan 1.4 shi ne a hanzarta kawo karshen tarzomar da ake yi a yankin Hongkong, ta yadda za a dawo da doka da oda a yankin.

An labarta cewa, a 'yan kwanakin baya, dimbin Sinawa wadanda suke zaune ko suke karatu a sassa daban daban na duniya, kamar kasashen Burtaniya da Australiya, sun yi zanga-zanga, inda suke goyon bayan matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan batun yankin Hongkong. Wannan ya sa wasu gwamnatocin kasashe suka nuna damuwa cewa, hukumomin kasar Sin dake sassa daban daban na duniya ne suka shirya irin wadannan zanga-zanga. Game da wannan tambaya, Mr. Geng Shuang yana mai cewa, "A kwanakin baya, wasu Sinawa dake zaune a sassa daban daban na duniya sun shirya zanga-zangar lumana, inda suka bayyana fatansu na nuna goyon bayan dinkuwar kasar Sin baki daya waje guda, da fatan ganin an hanzarta tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Hongkong. Bugu da kari, sun bayyana bakin cikinsu kan wasu kalaman yunkurin raba yankunan kasar Sin da bata sunan kasar. Sun yi haka ne kamar yadda ya kamata, kuma abubuwa ne da kowa ya sani. Muna fatan Sinawa wadanda suke zaune a ketare su mai da hankali ga tsaron kansu a lokacin da suke bayyana niyyarsu ta kishin kasa bisa doka." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China