Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 15 sun mutu sanadaiyyar harin Boko Haram a Borno
2019-12-15 16:40:22        cri
Kimanin mutane 15 ne suka mutu sakamakon harin da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka kaddamar a wani garin dake jihar Borno, a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Usman Zannah, dan majalisar wakilai ta tarayyar daga jihar Borno, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa mayakan kungiyar Boko Haram cikin wasu motoci 11 sun afkawa garin Magumeri, mai tazarar kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, da yammacin ranar Alhamis da ta gabata inda suka yi mummunar barna a garin.

A cewar Zannah, daga cikin mutanen da suka mutu har da jami'an tsaron sa kai su 8, da mazauna yankin 6, sai kuma wani jami'in tsaro guda. An gano gawarwakinsu a ranar Juma'a kwana guda bayan kaddamar da harin.

Mayakan sun yiwa garin dirar mikiya dauke da manyan bindigogin kakkabo jiragen sama da wasu manyan makamai.

Ba'ana Liman, wani mafarauci ne a yankin, ya ce maharan sun shafe sa'o'i da dama suna musayar wuta da 'yan farautar wadanda ke amfani da kananan bindigogi kirar hannu.

Rundunar sojojin Najeriya ba su tabbatar da faruwar harin ba. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China