Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikatan kamfanin gine gine 3 a tsakiyar Najeriya
2019-12-11 09:54:08        cri
Jami'an 'yan sanda a Najeriya sun bayyana cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma'aikatan kamfanin gine gine su uku kana biyu daga cikinsu 'yan kasashen waje ne a wani kauye dake jihar Naija a shiyyar tsakiyar Najeriya.

Daga cikin ma'aikatan uku da aka yi garkuwa da su a ranar Litinin, mutum guda ne kawai aka tabbatar dan Najeriya ne dake aiki da kamfanin gine gine na Triacta, wani kamfanin kasar Lebanon a kauyen Kogo na karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija.

'Yan sandan sun ce ma'aikatan suna gudanar da aikin gina hanyar mota ne a yankin yayin da 'yan bindigar suka yi awon gaba da su.

Adamu Usman, babban jami'in 'yan sandan jjhar Naija, ya fadawa 'yan jaridu cewa, 'yan bindigar sun yi badda kama ne da zummar sojoji.

A cewar Usman, suna sanye da kayan sojoji kuma suna haye kan babura sama da guda 20 inda suka afkawa harabar kamfanin gine ginen.

Jami'in 'yan sandan ya ce, 'yan bindigar sun fi karfin jami'an 'yan sandan dake aiki a wajen inda suka yi musayar wuta da 'yan sandan a kan Babura kana suka yi awon gaba da ma'aikatan.

Ya ce tuni aka tura tawagar jami'an bincike domin ceto mutanen da aka yi garkuwar da su, kuma za su yi dukkan bakin kokarinsu domin ceto ma'aikatan ba tare da an jikkatasu ba, in ji jami'in 'yan sandan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China