Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin saman Najeriya sun tabbatar da hallaka mayakan Boko Haram 30
2019-12-12 10:25:18        cri
Kakakin rundunar sojojin sama a tarayyar Najeriya Ibikunle Daramola, ya ce dakarun rundunar sun hallaka a kalla mayakan kungiyar Boko Haram 30, tare da lalata sansanoninsu, ciki hadda wani sansanin kungiyar dake garin Parisu, da wata maboyar 'yan ta'addan dake garin Maloma, garin da ke makwaftaka da dajin Sambisa na jihar Borno, a arewa maso gabashin kasar.

Mr. Daramola wanda ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan, ya ce farmakin na ranar Talata, na da nufin kakkabe gyauran mayakan na Boko Haram daga wannan yanki, tare da datse musu damar kaddamar da hare-hare.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai ya sha fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da ayyukan kungiyar ta Boko Haram cikin kusan shekaru 10, inda a shekarar 2014 kungiyar ta yi garkuwa da 'yan mata da dama dake karatu a wata makarantar sakandare.

Burin kungiyar Boko Haram dai shi ne kafa abun da ta kira daular Islama, a kasar dake kan gaba wajen yawan al'umma a daukacin nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China