Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF: Dakarun tsaron sa kai a Najeriya sun 'yantar da yara 461 dake aiki karkashin su
2019-12-11 10:14:17        cri
Asusun yara na UNICEF, ya ce rundunar dakarun tsaron sa kai mai tallafawa yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ko CJTF, ta mika wasu yara su 461 dake aiki a karkashin rundunar ga mahukuntan jihar Borno.

UNICEF ta tabbatar da cewa, an mika yaran ne masu shekaru 12 zuwa 13 ga mahukuntan jihar Borno a birnin Maiduguri, bayan da yaran suka yi aikin yaki da kungiyar Boko Haram tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017.

An kafa rundunar CJTF ne a shekarar 2012, musamman domin tallafawa dakile hare-haren Boko Haram, ta kuma taka rawar gani wajen ba da kariya ga yankunan da suka sha fama da tashe-tashen hankulan 'yan ta'adda, inda a lokuta da dama suke korar 'yan Boko Haram zuwa dajin Sambisa da kuma yankunan tafkin Chadi.

Babban jami'in ofishin UNICEF a jihar Borno Geoffrey Ijumba, ya ce adadin yara kanana dake ayyuka masu alaka da tawagar CJTF a birnin Maiduguri da kewayen jihar ta Borno sun kai 3,737. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China