2019-12-12 10:22:50 cri |
Mohammed Aliyu, ya shaidawa manema labarai a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno cewa, an kame wadanda ake zargin ne yayin ssamame na wata daya a sassan jihar daban daban, a kuma lokuta mabanbanta.
Kwamishinan ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa, mafi yawan wadanda aka kama samari ne, don haka ya yi kira ga iyayen yara da su kara azama wajen sanya ido, da baiwa 'ya'yan su tarbiyya da ta dace, domin dakile yaduwar muggan laifuka tsakanin al'umma.
Daga nan sai ya jaddada kudurin rundunar 'yan sandan na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma, yana mai fatan samun cikakken hadin kai daga al'umma, ta hanyar samar da bayanai ga 'yan sanda domin tabbatar da nasarar tsaro a jihar. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China