2019-12-13 10:21:39 cri |
Nnamdi Omoni, kakakin hukumar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da mutuwar mutanen cikin wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal, babban birnin jihar, sai dai ya ce kawo yanzu hankula sun kwanta a yankin Chokocho da aka samu tashin hankalin.
Ya ce an kashe mutane 6 a yayin zanga zangar da ta barke da safiyar Lahadi inda ta bazu har zuwa wayewar garin Litinin, sabanin labarin da ake yadawa na mutuwar mutane 15, kuma ba'a kune ofishin 'yan sanda ba, kana ba wani fasinja da aka kaiwa hari ko aka hallaka, sabanin jita jitar da ake yadawa.
Yan sandan ba su bayyana masabbin zanga zangar ba, sai dai wani 'dan jaridar yankin ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa rigingimu tsakanin al'ummun yankin ne ya haddasa barkewar tashin hankalin.
Omoni ya ce bincike ne kadai zai tabbatarwa 'yan sandan gano masabbin kashe mutanen da kuma wadanda ke da hannu wajen tada rikicin. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China