Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yong ya kai ziyarar aiki a Lesotho
2019-12-15 16:35:54        cri

Mamban majalisar gudanarwa na kasar Sin Wang Yong wanda ke ziyarar aiki a Lesotho ya gana da firaministan kasar Thomas Motsoahae Thabane a Maseru, fadar mulkin kasar.

A ganawar tasu, Wang Yong ya nuna cewa, Lesotho sahihiyar abokiyar kasar Sin ne, ya jinjinawa matakin da kasar ke dauka na amincewa da kasar Sin daya tak a duniya, kuma yana fatan kasashen biyu za su kara hada kansu a bangaren tsare-tsaren raya kasa da kara mu'ammalar al'adu da kiyaye muradun kasashe masu tasowa cikin harkokin kasa da kasa bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ya yi imani cewa, dangantakar kasashen biyu za ta kai ga wani sabon matsayi bisa kokarin da suke yi tare da samun ci gaba mai armashi.

A nasa bangare, Thomas Motsoahae Thabane ya bayyana cewa, dangantakar kasashen biyu na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, yana godiya da taimakon da Sin take baiwa Lesotho ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma. Lesotho tana dora muhimmanci sosai kan dangantakar kasahen biyu, tana nacewa ga manufar kasar Sin daya tak a duniya da kara amincewa da juna a bangaren siyasa da zurfafa hadin kai a fannoni daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China