Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo yana yunkurin maida Amurka gaban kome ta hanyar kiyaye tsaro kan batun fasahar 5G
2019-12-05 16:10:03        cri
Shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar EU Zhang Ming ya rubuta a shafin yanar gizo na Politician na Turai a jiya cewa, bai amince da ra'ayin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, wanda ya zargi kasar Sin da ta gudanar da ayyukan leken asiri da kwace ikon mallakar ilmi, da sa kaimi ga kasashen Turai kada a yi hadin gwiwa da kasar Sin wajen raya fasahar 5G ba, Mr Zhang Ming yana mai jaddada cewa, hadin gwiwa da yin imani da juna hanya ce daya tilo mai dacewa.

Zhang Ming ya bayyana cewa, a ranar 2 ga wannan wata, Pompeo ya sake zargin kasar Sin da kamfanin kasar, tare da gabatar da misalai da dama ba tare da tushe ba. Koda yake kasar Amurka ta yi matsin lamba a fannin siyasa ko bada labarai da dama game da kasar Sin, babu wata kasa ko wani mutum dake da shaidun cewa kamfanin Huawei ya kawo barazanar tsaro.

Zhang Ming ya jaddada cewa, a lokacin da wata sabuwar fasaha ta fito, ya kamata a maida hankali ga batun tsaro. A halin yanzu, kasa da kasa suna kokari wajen tabbatar da tsaro kan fasahar 5G. kuma ya kamata a yi hadin gwiwa da yin imani da juna don kafa tsarin fasahar 5G mai aminci yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China