Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwan rashin kunya da 'yan siyasan Amurka suka yi sun nuna mugun nufinsu
2019-11-27 20:19:14        cri

Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Laraba cewa, wasu 'yan siyasan kasar Amurka da jami'anta su kan bata sunan kasar Sin, abubuwa rashin kunya da suka yi sun nuna ainihin mugun nufinsu da kuma makarkashiyarsu ta fannin siyasa.

Rahotanni na cewa, a ranar 25 ga wata, Richard Grenell, jakadan Amurka da ke kasar Jamus ya sanar da cewa, an kasa kwatanta kasar Sin da kasar Amurka a fannin da'a.

Dangane da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a Beijing cewa, har kullum kasar Sin na himmantuwa wajen wanzar da zaman lafiya a duniya, tana ba da gudummawa wajen bunkasar duniya, tana kuma kiyaye tsarin kasa da kasa. Duk wani yunkurin da ake yi na musunta tsarin gurguzu na kasar Sin da kuma rusa alaka a tsakanin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kasar Sin ba zai yi nasara ba. Karya, sau dubu karya ce, kuma fure take ba ta 'ya'ya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China