Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin kudancin Afrika ya samu ruwan sama mafi karanci tun bayan shekarar 1981
2019-06-04 11:38:44        cri

Jimilar ruwan sama a yankin kudancin Afrika, a lokacin damina daga watan Oktoban 2018 zuwa Maris din 2019, ita ce mafi karanci a cikin shekaru 38

Sanarwar da aka karanta yayin taron Ministocin kula da harkokin gona da wadatar abinci da kiwon kifi da dabbobi da tsirran ruwa na kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC a birnin Winhoek na Namibia, ta ce alkaluman nazarin ruwan sama sun nuna cewa, jimilar ruwan da aka yi a tsakanin wancan lokaci, ya zama mafi karanci tun bayan shekarar 1981, a sassan kasashen Angola da yammacin Botswana da Comoros da arewacin Namibia da yammacin da tsakiyar Afrika ta Kudu da Lesotho da yammacin Zambia da kuma Zimbabwe.

Sanarwar ta ce karancin ruwan sama ya yi mummunan tasiri kan abincin dabbobi da dabbobin kansu, da kuma ruwan amfani ga dan Adam da harkokin gona da sauran amfani, lamarin da ta ce sun tabarbare a yammacin yankin.

Sai da kasashe 3 na kungiyar SADC suka ayyana dokar ta baci kan fari, saboda karancin ruwan sama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China