Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A karon farko an mika Jirgin saman dakon kaya kirar Morden Ark 600F na kasar Sin
2019-08-29 11:34:54        cri

Kwanan baya, rukunin masana'antun kera jigaren sama na kasar Sin (AVIC) ya mika wani jirgin saman dakon kaya kirar Morden Ark (MA) 600F ga kamfanin sufurin kayayyaki ta jiragen sama na kasar Sin, wannan shi ne karo na farko da aka fara amfani da wannan nau'in jirgin sama a duk duniya.

Kawo yanzu dai, Rukunin AVIC ya riga ya mika jiragen sama kirar MA nau'o'i daban daban fiye da 100 zuwa ga kasashe 18 daga nahiyoyi 4, wadanda suka yi jigilar fasinjoji fiye da miliyan 12 a kan hanyoyin jirgin sama kusan 300 yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, Rukunin AVIC ya horar da kwararru fiye da 3000 masu kula da ayyukan tafiyar da harkokin jirgin sama da gyara jirgin da ma tuka shi. Yadda aka mika jirgin saman dakon kaya kirar MA 600F ya alamta cewa, tsarin kera jiragen sama nau'o'i daban daban ya kyautata sosai, wanda ya hada da jirgin sama na jigilar fasinjoji, da na dakon kaya, da sauransu.

Ya zuwa watan Nuwamban shekarar bara, masu sayayya 11 sun riga sun daddale yarjeniyoyin sayen sabon nau'in jirgin sama kirar MA 700 guda 285.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China