Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: Yawan wadanda Ebola ta hallaka a DRC ya kai 2,209
2019-12-13 10:45:50        cri
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta ce yawan mutanen da cutar Ebola ta hallaka a jamhuriyar dimokuradiyyar Congo ya karu zuwa 2,209.

Kungiyar mai kasashe mambobi 55, ta ce bisa rahotonta na baya bayan nan game da yaduwar cutar ta Ebola, ya zuwa ranar 8 ga watan Disambar nan, an samu karuwar mutane 59 da cutar ta hallaka, cikin jimillar mutum 2,150 da suka mutu sakamakon kamuwa da ita tun daga ranar 13 ga watan Oktoba da ya gabata.

Kungiyar AU wadda ke samar da tallafi ga yakin da ake yi da wannan cuta, karkashin cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka ko CDC a takaice, ta ce ya zuwa ranar 8 ga watan Disamban nan, adadin wadanda aka tantance sun kamu da cutar ya kai mutum 3,327.

To sai dai kuma AU ta ce cikin wannan adadi, mutane 1,087 sun farfado bayan shan fama da cutar mai saurin kisa, wanda hakan ya nuna tsayawar alkaluman kisan da cutar ta yi kan kaso 67 bisa dari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China