Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Afirka sun jaddada muhimmancin yaki da ta'addanci domin bunkasa ci gaban nahiyar
2019-12-12 10:24:02        cri
Shugabannin kasashen Afirka da wasu wakilan sassan kasa da kasa, sun jaddada muhimmancin zage damtse ga aikin yaki da ta'addanci, da tabbatar da tsaro, a matsayin hanyar wanzar da ci gaban nahiyar.

An dai gabatar da wannan shawara ne a jiya Laraba, yayin kaddamar da taron yini biyu, na tattauna dabarun wanzar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka, taron da ya gabata a birnin Aswan na kasar Masar.

Taron na Aswan dai zai maida hankali ga batutuwa da suka kunshi sake gina yankuna bayan tashe-tashen hankula, da raya ilimi, da sauyin yanayi, da kuma ci gaba mai dorewa a Afirka.

Da yake gabatar da jawabin bude taron, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen aiwatar da matakan yaki da ta'addanci a dukkanin sassan duniya.

A nasa tsokaci kuwa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ne da a maida hankali ga kandagarkin tashe-tashen hankula a Afirka, yana mai cewa, nahiyar na bukatar karin zuba jari a fannin raya ilimi, wanda ke share fagen samun rayuwa mai nagarta ga daukacin al'umma.

Shi kuwa shugaban jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou cewa ya yi, muddin babu tsaro, to kuwa babu wani ci gaba na a zo a gani da zai samu a kasashen nahiyar.

Sauran shugabannin Afirka da suka halarci taro na Masar sun hada da na Chadi, da Senegal, da kuma wakilai daga Amurka, da Birtaniya, da MDD.

(Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China