Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar AU ta yi kira ga mambobin ta da su hanzarta amincewa da kundin bayanai game da yarjejeniyar shige da fice
2019-11-10 15:57:24        cri
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta yi kira ga mambobin ta, da su hanzarta tabbatar da amincewa da kundin bayanai, game da yarjejeniyar shige da fice tsakanin kasashen nahiyar.

An yi wannan kira ne yayin taron ministoci na kasashe mambobin kungiyar 55, wanda ya gudana a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Da take tsokaci game da wannan batu, kwamishiniyar AU mai kula da harkokin jin dadin al'umma Amira Elfadil, ta ce kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar ta AU, su amince da kundin, kamar yadda yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar ko AfCFTA ta tanada. Ta ce, kaurar jama'a barkatai daga wasu sassan nahiyar zuwa sauran yankuna na duniya, da karuwar masu gujewa muhallan su, na zama wani babban kalubale ga kasashen Afirka.

Kasashe 33 ne dai suka sanya hannu kan yarjejeniyar ta AfCFTA, kana 4 daga ciki suka mikawa AU takardun nuna cikakkiyar amincewa da ita. Wadannan kasashe dai su ne Rwanda, da jamhuriyar Nijar, da Mali da kuma Sao Tome da Principe.

Bisa tsarin yarjejeniyar, sai kasashe a kalla 15 sun tabbatar da amincewar su da ita kafin ta fara aiki gadan gadan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China