Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta nuna damuwa kan yadda Birtaniya ke ci gaba da mulkin mallaka ga Chagos Archipelago
2019-11-24 15:58:38        cri
Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU) Moussa Faki Mahamat, ya nuna damuwa matuka game da yadda Birtaniya ke ci gaba da mulkin mallaka ga yankin Chagos Archipelago.

Wata sanarwar da AU ta fitar da yammacin Juma'a ta bayyana cewa, shugaban na AU ya bayyana matukar damuwa game da yadda kasar Birtaniya ke ci gaba da yiwa Chagos Archipelago mulkin mallaka, wanda hakan ya saba da kudirin MDD mai lamba 73/295 wanda aka amince da shi a ranar 22 ga watan Mayun 2019, inda kasashen duniya suka bukaci Birtaniya ta janye ba tare da gindaya wasu sharruda ba cikin watanni 6 daga ranar da aka amince da kudurin, wanda ya kare a ranar 22 ga watan Nuwambar shekarar 2019.

Shugaban kungiyar ta Afrika mai mambobi kasashe 55 ya ce MDD ta amince da kudurin mai lamba 73/295 ne bayan da kotun duniya ta zartar da hukunci a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekarar inda ta nuna halascin raba yankin Chagos Archipelago daga kasar Mauritius a shekarar 1965.

Mahamat ya jaddada goyon bayan AU ga kasar Mauritius da ta tabbatar da baiwa Chagos Archipelago yancin kanta, wanda hakan ya yi daidai da dokokin kungiyar AU na tabbatar da 'yancin cin gashin kai, da ikon mulkin kasa, wanda ya dace da manufofin AU. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China