Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta musanta rahoton dake cewa Kasar Sin na leken asiri a hedkwatarta
2019-11-16 16:01:07        cri
Wani babban jami'in Tarayyar Afrika AU, ya yi watsi da rahotannin kafefen yada labarai dake cewa, kasar Sin ne leken asiri a hedkwatar Tarayyar tare da daukar muhimman bayanai daga rumbun adana bayanai na hedkwatar.

Victor Harison, kwamishinan AU mai kula da harkokin tattalin arziki, ya bayyanawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, yana girmama martanin da Shugaban hukumar tarayyar, Mousssa Faki Mahamat ya yi a bara, inda ya yi watsi da rahoton jaridar Le Monde ta Faransa, wadda ta yi ikirarin cewa, kasar Sin na leken asiri a cibiyar tarukan AU da ta gina tare da ba da ita kyauta ga Tarayyar a shekarar 2012.

A cewar Victor Harison, shugaban hukumar AU ya riga ya mayar da martini kan batun, kuma yana girmama amsar da shugabansa ya bayar.

A bara ne Moussa Faki Mahamat, ya shaidawa manema labarai cewa, rahotannin zargi ne kawai da basu da tushe, yana mai jaddada cewa babu abun da zai lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Tarayyar Afrika, kuma irin wadannan rahotanni ba za su iya illata dangantakar ba.

Har ila yau, Victor Harison ya ce AU da Sin na more kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsu, inda ginin ofishin tarayyar da cibiyar tarukanta ke zaman misali na dagantakar.

Shi ma da yake watsi da jita-jitar, Liu Yuxi, shugaban tawagar Sin a AU, ya shaidawa manema labarai cewa, an gina dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ne bisa girmamawa da moriyar juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China