Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a yi kokarin magance matsalolin tsaro dake tasowa a Afrika
2019-11-12 14:03:00        cri
Kwamishinan Tarayyar Afrika mai kula da harkokin tsaro da zaman lafiya, Smail Chergui, ya jaddada bukatar a yi kokarin shawo kan barazanar tsaro dake tasowa a nahiyar Afrika.

Smail Chergui ya ce yanayin tsaro mai sarkakiya da sauye-sauyen tsaro a nahiyar Afrika na bukatar aiki mai dorewa da zai gina dabi'ar hakuri da juna da zaman lafiya.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin taron hukumar dake rajin wanzar da zaman lafiya na MDD da kwamitin tsaro na AU, a hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa na Habasha.

Smail Chergui, ya jaddada bukatar zurfafa hadin gwiwar AU da MDD wajen magance kalubalen tsaro da zaman lafiya dake illa ga kwanciyar hankali a Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China